Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya raba kayan abinci da sauran kayan buƙatu ga gidaje 447, da sansanonin ‘yan gudun hiira a Dolari da ke yankin ƙaramar hukumar Konduga.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce ita ce gina sabbin gidajen domin sake tsugunar da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a yankin.
Sanarwar ta ce sabuwar unguwar da aka gina ta ƙunshi makaranta da asibiti da tashar samar da ruwan sha.
”Mutanen da aka sake tsugunar da su a sabbin gidajen sun hada magidanta 197 daga sansanin ‘yan gudun hijira na Kawar Maila, da magidanta 250 daga sansanin ‘yan gudun hiira na Dolari”, in ji sanarwar.
Kayayyakin da aka raba wa mutanen sun haɗa da kayan abinci da tabarmi da barguna da tufafi.
Yayin da yake jawabi a wajen raba kayan, gwamnan Zulum ya ce gwamnatin jihar ta samar da kayyakin buƙatun ne don tallafa wa mutanen da aka sake tsugunarwar su samu damar fara sabuwar rayuwa a wurin.