Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya ya sauya wa wasu manyan hafsoshin rundunar sojin ƙasar wuraren aiki.
Manyan hafsaoshin sojin da sauyin wurin aikin ya shafa ba su wuce muƙaman Kanal ba.
Za su kula ne da wasu muhimman wurare a yankin rainon Ingila mai fama da rikicin ‘yan a-ware da ke rajin kafa ƙasar Ambazoniya, da kuma ta arewacin ƙasa inda rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita jama’a.
A makon jiya ne Ministan tsaro ya shugabanci wani taro na musamman domin tattauna lamarin taɓarɓarewar tsaron da ƙasar take fama da shi.


