fidelitybank

Sugaban Sudan ta Kudu ya kai ziyara Rasha

Date:

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir yana ziyara a birnin Moscow domin tattaunawa da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin.

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da Rasha da ƙasashen yammacin duniya ke ƙoƙarin neman goyon bayan ƙasashen Afirka bayan mamaye Ukraine.

Mr Kiir ya isa babban birnin ƙasar Rasha ne a ranar Laraba inda mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Andrey Rudenko Yurevich ya tarbe shi, kamar yadda sanarwar fadar shugaban ƙasar ta bayyana.

Ofishin Mista Kiir ya ce ganawar da zai yi da shugaba Putin a ranar Alhamis, za ta tattauna kan batutuwan da suka shafi ci gaban dangantakar ƙasashen biyu a fannoni daban-daban.

Ta kara da cewa ziyarar na da nufin kara karfafa hulɗar diflomasiyya da kuma haɗin gwiwa a ɓangaren ciniki da zuba jari da kuma tsaro.

Sanarwar ta kara da cewa shugabannin biyu za su tattauna batun ɗage takunkumin hana sayar da makamai da kuma takunkumin da aka kakaba wa wasu mutane a Sudan ta Kudu.

A watan Mayun da ya gabata ne dai Rasha ta kaurace wa kuri’ar da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi na sabunta takunkumin da aka kakaba wa Sudan ta Kudu, da suka haɗa da kwace kadarori da hana zirga-zirga da kuma sanya takunkumin makamai.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp