Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar tsaro ta Eastern Security Network, ESN, da laifin kashe wani sufeton ‘yan sanda a ofishin ‘yan sanda na Ndiegoro da ke Aba, jihar Abia.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na daren ranar Talata a hanyar Ohanku, mahadar Iheorji a garin Aba.
A lokacin da lamarin ya faru, ‘yan sanda sun kashe biyu daga cikin maharan a fafatawa da suka yi.
NAN ta bayyana cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Abia, SP Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ogbonna ya ce, wasu ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Ndiegoro suna sintiri a kewayen Iheorji lokacin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar ESN/IPOB ne suka kai musu hari.
“A yayin da aka yi musayar wuta da bindiga, daya daga cikin ‘yan sandan ya rasa ransa.
“Yayin da suka harbe dan sandan, sun kuma karbo bindigar AK-47 na ‘yan sanda,” in ji shi.