Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei Bona Malwal da Kakakin Majalisar Dokoki ta riƙon ƙwarya ta Sudan ta Kudu, Rt. Hon. Jemma Nunu Kumba da kuma wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Guang Cong sun ziyarci ofishin jakadancin Najeriya da ke Juba domin miƙa gaisuwar ta’aziyya da bayyana jimami da alhininsu kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari.
Ambasada Akuei Bona Malwal ya miƙa wasikar ta’aziyyar ne a madadin shugaban ƙasar, Salva Kiir Mayardit, zuwa ga Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu.
Mista Guang Cong ya kuma cewa za a riƙa tunawa da Buhari a matsayin wanda ya tsaya tsayin daka wajen haɗin kai tsakanin ƙasashe da kuma yaƙi da cin hanci.
A nasa ɓangaren, muƙaddashin Jakadan Najeriya a Sudan ta Kudu, Tukur Yahaya Maigari, ya nuna godiya bisa nuna tausayawa da zumunci, yana mai cewa Buhari jagora ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga ƙasa, kuma wannan ziyara ta nuna kyakkyawar dangantaka da mutunta juna tsakanin ƙasashen biyu.