Dan wasan gaban Inter Miami Luis Suarez ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasar Uruguay wasa.
Suarez ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai jiya litinin, yana mai cewa zai fice daga wasannin kasa da kasa bayan wasan da tawagarsa ta buga da Paraguay a gasar cin kofin duniya a ranar Juma’a.
Tsohon dan wasan gaban Liverpool da Barcelona ya tashi a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a tarihin kasar Uruguay inda ya zura kwallaye 69 a wasanni 142 cikin shekaru 17.
“Babu wani abin alfahari da kai fiye da sanin lokacin da ya dace na yi ritaya, kuma na yi sa’a ina da yakinin cewa na yi ritaya daga buga wa kasar wasa saboda ina so in dauki mataki a gefe.
“Ina da shekaru 37 kuma na san cewa yana da matukar wahala a iya zuwa gasar cin kofin duniya na gaba. Yana ƙarfafa ni sosai cewa zan iya yin ritaya ba don raunin da na ji ya yi mini ritaya ba, ko kuma in daina kiran sa,” in ji Suarez.
A watan Fabrairun 2007 ne Suarez ya buga wa Uruguay wasa a wasan da suka doke Colombia da ci 3-1.