fidelitybank

Suarez da Cavani sun shiga tawagar Uruguay da za su je Qatar

Date:

Tsoffin ‘yan wasan gaba Luis Suarez da Edinson Cavani na shirin buga gasar cin kofin duniya ta Fifa karo na hudu a jere bayan an sanya sunayensu cikin ‘yan wasa 26 na Uruguay da za su wakilci kasar a gasar a Qatar.

Tsohon dan wasan Liverpool Suarez, mai shekara 35, yana taka leda a kungiyar Nacional ta Uruguay.

Tsohon dan wasan Manchester United Cavani, mai shekara 35, ya zura wa Valencia kwallaye hudu a kakar wasa ta bana amma a halin yanzu yana murmurewa daga raunin da ya samu a idon sawunsa.

Mai tsaron baya Diego Godin, mai shekaru 36, yana cikin gogaggun tawaga.

An zabi babban dan wasan baya Ronald Araujo na Barcelona duk da cewa an yi masa tiyata a cinyarsa a watan Satumba.

Uruguay tana rukunin H tare da Koriya ta Kudu da Portugal da Ghana.

tawagar Uruguay:
Masu tsaron gida: Fernando Muslera (Galatasaray), Sergio Rochet (Nacional), Sebastian Sosa (Independiente)

Masu tsaron baya: Jose Maria Gimenez (Atletico Madrid), Sebastian Coates (Sporting CP), Diego Godin (Velez Sarsfield), Martin Caceres (LA Galaxy), Ronald Araujo (Barcelona), Guillermo Varela (Flamengo), Jose Luis Rodriguez (Nacional), Mathias Olivera (Napoli), Matias Vina (Roma)

‘Yan wasan tsakiya: Lucas Torreira (Galatasaray), Manuel Ugarte (Sporting CP), Matias Vecino (Lazio), Rodrigo Bentancur (Tottenham Hotspur), Federico Valverde (Real Madrid), Facundo Pellistri (Manchester United), Nicolas De La Cruz (River Plate).

Masu wasan gaba: Agustin Canobbio (Athletico Paranaense), Facundo Torres (Orlando City), Giorgian De Arrascaeta (Flamengo), Maxi Gomez (Trabzonspor), Luis Suarez (Nacional), Edinson Cavani (Valencia), Darwin Nunez (Liverpool)

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp