Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya danganta kalubalen da Najeriya ke fuskanta ga ‘yan kasar.
Da yake jawabi a gidansa da ke Bamaina a yayin bikin azumin watan Ramadan a ranar Lahadi, Lamido ya mayar da martani kan kiraye-kirayen kafa sabuwar jam’iyyar siyasa domin kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Ya ce ’yan Najeriya sun yanke shawarar fitar da jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP daga mulki, suka kawo APC ba tare da tunanin illar da hakan zai iya haifarwa ba.
“Kamar yadda na sha fada, ‘yan Najeriya ba su da masaniya game da Tinubu, kwararre ne kan yaudara da son kai,” in ji Lamido.
Kalaman nasa sun biyo bayan kiran da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi, inda ya bukaci jiga-jigan jam’iyyar adawa da su hada kai a karkashin jam’iyyar SDP domin ceto Najeriya daga hannun gwamnati mai ci.
Lamido, ya yi watsi da ra’ayin, yana mai cewa motsin rai da fushi kadai ba za su iya kayar da Shugaba Tinubu ba.
“Ba za ku iya kalubalanci Tinubu da fushi, kwadayi, ƙiyayya, hassada, ko mugunta ba, shi ne gwanin duk wannan,” in ji Lamido. “Manufar gaskiya da kishin kasa ne kawai za su iya fuskantarsa yadda ya kamata.”
Ya kuma bukaci ‘yan siyasa da a da su PDP su dawo jam’iyyar, yana mai jaddada cewa babu kunya a sake haduwa da ‘yan siyasar da suka yi nasarar mulkin kasar nan a tsakanin 1999 zuwa 2015.
Ya kara da cewa “Lokacin da al’umma ke fuskantar matsaloli, shugabanninta kada su bari korafe-korafensu su shafi hukuncinsu.”