Babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (SSS), Yusuf Bichi, ya ce hukumar ta cire wani dan jarida, Lanre Arogundade, daga jerin sunayen da ake sawa sunansa na wajen bibiyarsa na tsawon shekaru 38.
Bichi ya bayyana haka ne a lokacin da wata tawaga daga cibiyar yada labarai ta kasa da kasa (IPI Nigeria) reshen Najeriya ta ziyarce shi a Abuja.
Sakataren IPI na Najeriya, Ahmed Shekarau, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ya ce, ziyarar wani bangare ne na ayyukan kungiyar da ke ci gaba da gudanar da ayyukan kare lafiyar ‘yan jarida da ‘yancin yada labarai a Najeriya.