‘Yan majalisar dokokin Sri Lanka sun zaɓi firaminista Ranil Wickremesinghe a matsayin sabon shugaban kasar, duk da rashin amincewar jama’a.
Mista Wickremesinghe na fuskantar aikin jagorantar kasar daga durkushewar tattalin arziki da kuma maido da zaman lafiya bayan shafe tsawon watanni ana zanga-zanga.
Ya doke babban abokin hamayyarsa Dullus Alahapperuma wanda ya samu ƙuri’u 82 a kacal.
A makon da ya gabata ne tsohon shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga kasar.
Yanzu haka yana neman mafaka a Maldives da Singapore bayan dubban masu zanga-zanga sun mamaye gidansa da wasu gine-ginen gwamnati, suna masu kira da ya yi murabus.
Sun kuma yi kira da Mista Wickremesinghe ya yi murabus bayan nada shi firaminista a watan Mayu.
Masu zanga-zangar sun kona gidansa na kashin kansa sannan kuma sun mamaye ofishin firaministansa da ke Colombo a zanga-zangar adawa da shugabancinsa.
Sri Lanka ta yi fama da talauci sosai, kuma tana fuskantar matsanancin karancin abinci, da man fetur da sauran kayan masarufi.