Akalla kasashe biyu ne suka samu tikitin shiga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA da ke gudana a New Zealand da Australia a shekarar 2023.
Kasashen biyu su ne Spain da Sweden.
Hakan na zuwa ne biyo bayan kammala wasannin da aka fafata a ranar Juma’a.
Spain ta lallasa Netherlands da ci 2-1.
Ita kuwa Sweden ta ci Japan 2-1.
A ranar Asabar ne za a yi sauran wasannin daf da na kusa da karshe.
Australia za ta kara da Faransa, yayin da Ingila za ta kara da Colombia.