Ƙasashen Sifaniya da Norway da kuma Ireland na shirin amincewa da ƙasar Falasɗinawa cikin mako mai zuwa.
Ƙasashen uku sun ce a ranar 28 ga watan Mayun da muke ciki za su amince da matakin.
Minista harkokin wajen Ireland, Micheál Martin, ya ce ”a yau mun bayyana ƙarara ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba za mu nuna goyon bayanmu game da ‘yancin tsaro da na mutuntawa da gashin kai ga mutanen ƙasashen Falasɗinu da Isra’ila”.
Firaministan Madrid, Pedro Sanchez, ya ce firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ”yayi ƙunnen ƙashi, inda yake ci gaba da kai hare-haren boma-bomai kan asibitoci da makarantu tare da azabtar da mata da ƙananan yara da yunwa da kuma tsananin sanyi”.
A nasa ɓangare firaministan Irelan, ya ce ”samun yancin ƙasashen biyu shi ne kawai mafita a ƙoƙarin samar da zaman lafiya”.
Ƙasashen duniya da dama sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa.
A farkon wannan watan ƙasashe 143 daga cikin ƙasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193, sun kaɗa ƙuri’ar amince da da Falasɗinu ta shiga cikin MDD, wani abu da ƙasa mai zaman kanta ne kawai ke samun damar haka.