fidelitybank

Son zuciya ne ya sa NNPP ta kayar da APC a Kano – Adamu

Date:

am`iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta ce, tana jin takaicin kayen da jam`iyyar NNPP ta yi mata a jihar Kano a zaben gwamnan da ya wuce.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya shaida wa BBC cewa, babban abin bakin ciki shi ne a ce sun rasa Kano.

Ya ce, “ Kamar Kano, a ce mun rasa Kano, to amma laifin wasu ne ya sa muka fadi a Kanon.”

Shugaban na APC, ya ce “ Akwai wadanda ba su yi abin da ya kamata ba, ga shi a yanzu ya sanya ‘ya’yan jam’iyar cikin wani hali saboda nasarar da jam’iyyar ba ta samu ba, bayan ga shi su sun yi duk abin da ya kamata su yi.”

Ya kuma ce, Kano tana cikin jihohin da suke bugun kirji su ce wannan tamu ce, domin duk abin da za su yi Kano na kan gaba a lissafinsu.

Ya ce, “ Saboda wasu abubuwa na son zuciya an samu a cikin wani hali domin bai kamata a ce mun rasa Kano ba, to amma duk abin da ya samu bawa da sanin Ubangiji.”

“ Sai da muka ja dukkanin gwamnonin jam’iyyar APC a jihohin Najeriya a kan a rage son zuciya tun kafin zabe, kuma muna ganin son zuciyar ne ya ja mana rashin nasara a jiha kamar Kano,” In ji shi.

Shugaban APCn, ya ce yanzu jira suke duk hayaniyar zabe ta lafa don za su dauki mataki a kan duk wanda ya yi wa jam’iyyar abin da bai dace ba.

Sanata Abdullahi Adamu, ya ce to amma duk da rashin nasara a Kano, suna gode wa Allah da Ya ba su nasara a zaben shugaban kasa da kuma a wasu jihohin.

Ya ce, “ Zaben ma da ake jira za a kammala a Adamawa da Kebbi, mu ne za mu ci in Allah Ya yarda har ma mu je mu yi guda.

nnn hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Har yanzu ina LP kuma ni ne zan iya saita Najeriya – Datti

Datti Baba-Ahmed, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a...

APC ta zama buhun kusa ta gaza a Najeriya – Amaechi

Tsohon gwamnan jihar Ribas, Chibuike Amaechi ya bayyana jam'iyyar...

An fara samun takun saka tsakanin Turkiyya da Najeriya a kan kungiyar Gulen

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta bukaci shugaban kasar...

Arziƙin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 a farkon 2025 – NBS

Tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 3.13 cikin...

Kamfanonin lantarki za su katse wutar lantarki saboda bashi

Kamfanonin samar da wutar lantarki, sun ce suna iya...

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...
X whatsapp