Shugaban yankin Somaliya da ke gabashin Habasha ya ce, mayaƙan ƙungiyar al-Shabab mai iƙirarin jihadi sama da 800 ne aka kashe a faɗan baya-bayannan.
An kashe mayaƙan ne biyo bayan wasu hare-hare da ba a saba gani ba da kungiyar ta kai wasu ƙauyuka a bakin iyakar Somaliya da Habasha.
Mustafa M. Omer ya faɗa a Juma’ar nan cewa an tsare aƙalla mayakan 100, amma ya ce, shi bai tabbatar da faruwar haka ba da idanunsa.
A hare-haren farko a karshen watan Yuli, kungiyar da ke da alaƙa da al-Qaeda ta ce ta kashe dakarun Somaliya da dama.
Jami’an yankin sun mayar da martani bayan haka da nasu hare-haren na haɗin gwiwa. In ji BBC.


