Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Justice Peter Umeadi.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ya caccaki burin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, yana mai cewa Obidient Movement ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ne.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, Dr Alex Obiogbolu, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya fitar ya yi ikirarin cewa APGA ta kasance babbar jam’iyyar siyasa ta uku a kasar.
Soludo, wanda ke ganin cewa babbar jam’iyyar adawa ba ta yi wa yankin Kudu maso Gabas adalci ba ta hanyar karkata shugabancinta zuwa Arewa, ya ce goyon bayan kowace jam’iyya na iya shafar damar APGA a zaben 2023.
Ya ce: “APGA ta kasance babbar jam’iyyar siyasa ta uku a Najeriya, idan aka yi la’akari da yawan kujerun da ta samu.
“APGA tana da gwamnan Jiha, ’yan majalisar dokoki ta kasa da kuma ’yan majalisun jiha.
“APGA ba ta daukar guguwar ‘Obidient Movement’ a matsayin barazana ga cimma burinta a 2023.
“LP da ‘Obidient Movement’ ‘yan PDP ne. Don haka babbar barazana ce ga PDP ba APGA ba”.
DAILY POST ta rahoto cewa Soludo, wanda ya lashe zaben gwamnan Anambra a watan Nuwamba, 2021, ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar APGA.