A wani bangare na kudirin gwamnatinsa na tabbatar da samun lafiya, gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya kaddamar da wani shiri na musamman na tsaftar muhalli a babban birnin jihar.
An gudanar da atisayen ne a shaharren kasuwar Eke Awka, karshen mako.
Ya bayyana cewa, atisayen na daga cikin kudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsafta da muhalli da kuma walwalar ‘yan kasa.
Ya ba da umarnin gudanar da aikin tsaftar muhalli a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
A yayin da yake bayyana cewa, tsafta na gaba da ibada, gwamnan ya ce, nan da kwanaki masu zuwa, za a cimma tsare-tsare na gwamnatinsa na sabunta biranen da ya dace da kyawawan ayyuka a duniya.
Gwamnan ya yabawa mazauna jihar, bisa goyon bayan da suke ba su, ya kuma yi kira gare su da su hada kai da gwamnatin sa, domin gudanar da ingantaccen muhalli.
Gwamna Soludo, ya bayyana cewa, ya dauki ‘yan kwangila 31, domin su taimaka wajen tsaftace jihar duk da cewa, ya yi kira ga ‘yan kasuwar da ke sayar da kayansu a kan titunan jihar da su shiga kasuwanni.