Kwamishinan yada labarai na jihar Anambra, Law Mefor, ya ce gwamnan jihar, Farfesa Chukwuma Soludo, bai bayyana aniyar tsayawa takara a karo na biyu ba.
Hakan dai ya sabawa rade-radin cewa Soludo na neman wa’adi na biyu a matsayin gwamna.
Mefor wanda ya zanta da manema labarai a ofishinsa a ranar Larabar da ta gabata, ya ce duk da cewa har yanzu gwamnan bai bayyana sake tsayawa takara a karo na biyu ba, za a shawo kan shi ya tsaya takara saboda bajintar da ya nuna.
Ya ce: “Soludo bai bayyana aniyar tsayawa takara a karo na biyu ba. Ya shagaltu da sanya manufofi a jihar don bunkasa jihar.
“Ina daya daga cikin wadanda za su sa shi ya tsaya takara, kuma idan ya yi takara, zan tabbatar ya yi nasara. Ya nuna kansa shi ne abin da mutanen Anambra suke so.
“Duk alamun suna son Soludo. Shi dan Anambra ta Kudu ne, kuma tsarin shiyya ya fifita shi. Tsarin shiyya-shiyya da muke da shi a Anambara shi ne mutum ya cancanci wa’adi na biyu.
“Idan Soludo ya fafata, na tabbata zai yi nasara domin ba zai gaya wa kowa cewa zai yi hakan ko ya yi hakan ba, gara ya nuna musu abin da ya yi.
“Soludo na da damar tsayawa takara karo na biyu. Masu cewa za su fafata da shi, su ne wadanda suka fafata da shi a lokacin da ba gwamna ba ne kuma ya ci su.
“Me ya sa kuke ganin ba zai sake lashe su ba, yanzu da yake da shaidar abin da ya yi wa mutanen Anambra?
“Soludo yana da tabbataccen nasarori, nagartattun nasarori a Anambra, kuma duk abin da ya kamata ya yi shi ne ya nuna wa mutanen Anambra katin sa don sake zabar sa a karo na biyu,” in ji Mefor.