fidelitybank

Sokoto: Mazauna Sabon Sara sun aike da wasikar baccin rai ga Buhari

Date:

Jama’ar yankin Sabon Birni a Jihar Sokoto sun aike wa Shugaba Muhammadu Buhari, wasikar nuna bacin ransu a kan irin kisan gillar da ‘yan ta’adda ke yi musu kusan kullum a yankin.

Shugabannin karamar hukumar, sun aike wa Buhari wasikar ce bayan ’yan ta’adda sun kashe akalla mutum 80 cikin dare daya a Jihar Sokoto.

Kisan na biyu na zuwa ne bayan wasu ’yan ta’adda sun tare wata mota a kauyen Gidan Bawa da ke jihar, inda suka kone fasinjoji sama da 40 kurmus.

Wasikar ta bayyana wa Buhari takaicinsu kan irin kisan gillar da a a ke yi, musamman a yankunan Isa, Sabon Birni, Goronyo da kuma karamar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara wadda ke makwabtaka da Jihar Sokoto.

Shugabannin yankin sun ce ’yan ta’adda masu biyayya ga kasungurmin dan bindigar nan, Bello Turji, na kai farmaki kan al’ummomin yankunan, inda suke yi wa mata fyade baya ga lalata dukiyoyin jama’a.

A baya jama’ar Sabon Birnin sun taba rubuta wa Shugaba Buhari wasika domin shaida masa irin mawuyacin halin da suke fuskanta a yankinsu.

Takaicin kisan gillar ya sa fusatattun mutane da zargin Buhari da rashin katabus a kan lamarin, sai ma tafiya Jihar Legas da ya yi a ranar Alhamis, domin halartar taron kaddamar da littafi.

Tuni dai mutane a kafafen sada zumunta suka shiga kira da a yi zanga-zanga tare da neman wa shugaba Buhari ya sauka daga mulki kan rashin kawo karshen matsalar tsaro da ta damu wasu yankuna, musamman na Arewacin Najeriya. Inji Aminiya.

 

breaking news in nigeria today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp