Sojojin Ukraine sun tabbatar da ƙwato wasu ƙauyuka biyar a yankin Kharkiv da ke Arewa maso Gabashin Ukraine, yayin da suke ci gaba da gumurzu da sojojin Rasha da ke ta ruwan bama-bamai a birnin.
Sojojin sun ce, za su cimma burinsu na fatattakar Rasha da ke birnin da ya kasance na biyu mafi girma a Ukraine.
Rahotanni na cewa, manyan makamai da kasashen yamma ke taimakawa kasar da su, sun soma tasiri a wannan yaki.
A yankin kudanci kuma, Rasha na ci gaba da zafafa hare-hare a yankin Donbas, sai dai har yanzu ba ta yi wani nasara ba, duk da luguden wutar da take yi babu kakautawa.
A Mariupol, an sake kwashe wasu fararan-hula 50 daga yankin Azovstal mai masana’antu a ranar Juma’a, amma ‘yan Ukraine na cewa ana karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta. In ji BBC.