Rasha ta shaida wa sojojin Ukraine na karshe da suka rage a birnin Mariupol da take yi wa ruwan bama-bamai cewa, za su tsira da rayukansu idan suka mika wuya cikin sa’o’i masu zuwa.
Moscow ta ce dakarunta sun kawar da duk wasu sojojin turjiya daga birnin, baya ga share baraguzai daga hanya.
Sanarwar da ma’aikatar tsaron Rasha ta fitar ta bayyana yanayin da ake ciki a a matsayin bala’i.
Ta ce, ta yi tayin mika makaman ne a wani mataki na nuna dattaku da mutunta rayuka.