Rundunar Sojin sama ta kasa, ta ce, jirgin yaƙinta ƙarƙashin rundunar Operation Hadarin Daji ya ƙaddamar da hare-hare ranar 18 ga watan Nuwamba kan maɓoyar wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga mai suna Mallam Ila a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin saman Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar ranar Lahadi ya ce an kai hare-haren ne kilomita tara daga gabashin ƙauyen Manawa a ƙaramar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara.
Sanarwar ta kuma tabbatar da kashe ‘yan fashin daji bakwai, yayin da shi Mallam Ila ya kuɓuta bayan ya samu munanan raunuka.
Mallam Ila na ɗaya daga cikin mutanen da rundunar ke nema saboda kusancinsa da fitattun shugabannin ‘yan ta’adda kamar su Bello Turji da Dan Bokoyo.
‘Yan ta’addan da ke ƙarƙashin dabar Turji da Bokoyo su ne ke yawan kai hare-hare a ƙaramar hukumar Shinkafi da wasu yankunan jihohin Zamfara da Kaduna da Niger da Kebbi da Sokoto,kamar yadda sanarwar ta bayyana.