Dakarun sojin sama, sun ƙaddamar da hare-hare kan wasu sansanonin ‘yan fashin daji a wasu yankunan ƙananan hukumomin jihar Kaduna, tare da kashe ‘yan fashin daji masu yawa.
A wata sanarwa da kwamishinan al’umuran tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan a fitar ya ce an kai hare-hare kan wasu sansanonin ‘yan fashin daji a wasu ƙauyuka da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi.
Ya ƙara da cewa a yayin wannan hari an samu nasarar kashe ‘yan fashin daji uku tare da kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su a sansanin”
”Haka kuma a Walawa da ke ƙaramar hukumar Giwa an kai farmaki kan wani sansanin ‘yan fashin da wasu yankunan a ƙaramar hukumar Chikun”, in ji Kwamishinan.
Haka kuma ya ce dakarun sojin saman sun hangi wasu ‘yan fashin kilomita hudu a arewa mao yammacin Godani, inda nan take aka kashe su.