fidelitybank

Sojojin sama sun kashe shugaban ‘yan bindiga a Zamfara

Date:

Rundunar sojin sama ta kasa da ke aiki a jihar Zamfara ta kashe wani shugaban ‘yan bindiga, wanda aka fi sani da Dogo Rabe da wasu ‘yan kungiyarsa sama da 45 a dazuzzukan Zamfara.

Jami’an rundunar sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a sansanonin ‘yan bindigar da ke tsakanin al’umomin Zurmi da Birnin Magaji a jihar Zamfara da Jibia a jihar Katsina, kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.

Kwanaki kadan kafin tashin bam din, an kai wani hari makamancin wannan a sansanin na wani sarkin ‘yan bindiga, Bello Turji da ke unguwar Fakai a jihar, inda aka kashe ‘yan bindiga a kalla 22, yayin da Turji ya tsere.

A cewar wata majiya daga yankin, Abdulbaqi Aliyu, harin na baya-bayan nan ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindiga a kalla 40 a yankin Birnin Magaji na jihar.

“Rundunar sojin saman Najeriya ta kai farmaki a dajin Sabon Birini Dan Ali, a karamar hukumar Birini Magaji, wanda ya yi sanadin kashe ‘yan fashin sama da 40,” inji shi.

An kai harin ne a lokacin da aka ce gungun na lodin shanun da aka sace.

“Ba a bayyana adadin mutanen da aka kashe a wannan farmakin ba saboda ‘yan bindigar sun taru a gidan Dan Karami domin yin taro. Babu tabbas ko yana cikin wadanda aka kashe,” inji majiyar.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga Abdul Olaitan, kakakin rundunar sojin sama a jihar Katsina yayin da bai amsa kiran manema labarai ba.

daily post newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp