fidelitybank

Sojojin Sama sun kama mai garkuwa da mutane a Kano

Date:

Jami’an rundunar sojin saman Najeriya NAF, sun kama wani matashi dan shekara 35 da ake zargi da yin garkuwa da mutane mai suna Isah Abdul, wanda ake kyautata zaton yana da hannu wajen yin garkuwa da mutane da dama a bayan garin Kano.

A cewar NAF, an kama mutumin ne a ranar 19 ga watan Fabrairun 2024 da misalin karfe 6.30 na yamma a wani aiki na hadin gwiwa bayan samun bayanan sirri kan maboyar wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne da kungiyarsa.

Air Vice Marshal Edward Gabkwet, Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na Rundunar Sojojin Saman Najeriya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne a Durbundai a karamar hukumar TakaiĀ  a jihar Kano.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa Isah Abdul da ā€˜yan kungiyarsa ne suka yi garkuwa da wani Yakubu Ibrahim Tagaho, wanda aka fi sani da ā€œSarkin Noman Gaya,ā€ a ranar 6 ga Afrilu, 2023, daga gidansa da ke kauyen Tagaho a karamar hukumar Takai.

Ya kara da cewa, bayan wata guda an sako wanda aka kashen bayan an biya kudin fansa naira miliyan 30.

ā€œA cikin watan Disambar 2023, wannan mai laifin ya sace ā€˜yan uwa mata 2 da wasu 3 a kauye daya sannan ya sake su bayan karbar makudan kudin fansa.

Sanarwar ta kara da cewa, “Haka kuma yana da alhakin wasu ayyukan garkuwa da mutane saboda yana da alaka mai karfi da wasu sannnan kungiyoyin masu garkuwa da mutane kamar kungiyar Danbul Fulaku da ke aiki a karamar hukumar Takai.”

Sanarwar ta bayyana cewa a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun rundunar sojin saman Najeriya, yayin da ake ci gaba da bincike.

Sanarwar ta kara da cewa nan ba da jimawa ba za a mika shi ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da shari’a.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ę“ansandan jihar Kaduna, sun buʙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ʙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ā€˜Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ʙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ā€˜yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp