Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya sha alwashin gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifukan yaki a Ukraine a gaban kuliya.
Ukraine na aiki tare da Tarayyar Turai da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya don tabbatar da cewa an gudanar da cikakken bincike kan laifukan yaki a Bucha da sauran garuruwan Ukraine, in ji shugaban na Ukraine a wani sakon bidiyo.
“Wadanda ke da alhakin ya kamata a hukunta su kan laifukan.
Ya kara da cewa, “Lokaci zai zo da kowane dan kasar Rasha zai san gaskiya game da wanene daga cikinsu ya kashe ‘yan kasarsa.”
Ukraine ta ce, ta gano gawarwakin fararen hula 410 daga garuruwan Bucha da Irpin da ke wajen birnin Kiev bayan janyewar sojojin Rasha.
Ukraine, tare da manyan kasashen duniya da dama, sun ce, sojojin Rasha sun yi kisan kiyashi.
Moscow ta ce ba ta da alaka da kashe-kashen, kuma ta kira hotunan “karya”.
Shugaban na Ukraine ya ce, a tafiyarsa zuwa Irpin da Bucha, “An lalata su ne kawai.”
“Ina jin tsoron cewa ,sojojin Rasha a yanzu suna kokarin boye bayanan laifukan da suka aikata,” in ji shi.


