Sojojin Rasha sun sace magajin garin Kudancin birnin Dniprorudne, in ji ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba.
Yevhen Matveyevshi ne magajin gari na biyu da aka yi zargin sojojin Rasha sun sace cikin kwana uku, bayan magajin garin Melitopol da aka sace a ranar Juma’a.
Kuleba ya ce, “Salon yakin Rasha a kwai zalinci ciki sun sace Matveyev”.
Wannan dai shi ne magajin gari na biyu da Rasha ta yi garkuwa da su a Ukraine.