Ukraine ta ce sojojin Rasha sun fatattaki rundunoninta daga tsakiyar birnin Severodonetsk a yankin da fada ya yi zafi a baya-bayan nan.
Sojojin Ukraine sun ce ana ci gaba da gwabza fada a birnin amma wani jagoran mayaƙan sa kai na Rasha ya ce, ƴan Ukraine din da ke wajen a yanzu suna da zaɓin miƙa wuya ko mutuwa.
Ukraine ta bayyana cewa Rasha ta kara shigar da karin makamai da motoci masu sulke zuwa wasu yankuna masu makwabtaka a yunkurinta na yi wa dakarun Ukraine kawanya.
A cewar wakilin BBC, yaki ne ake kan tituna kuma yana ci gaba da ƙazanta kuma iya abin da muka sani, kowane bangare na tafka asara.
Rasha na amfani da damarta ta samun atilari wajen kai hare-hare a Ukraine.