Dakarun Rasha da ke mamayar Ukraine, sun sake kutsawa karin wasu biranen kasar, inda suka zafafa hare-hare babu kakkautawa.
Rahotanni daga wajen birnin Kyiv na cewa, a na ta gwabza luguden wuta ta ko ina da harba makaman roka.
Oleksandr Merezhko dan majalisa ne karkashin jam’iyya mai mulki, ya ce, sojin Rasha sun fara sauya salon yakin.
Ya ce, alamu sun nuna sojin Rasha na sauya salo, sun gane su na da matsalar kayan masarufi, sannan yawanci sun fara dimaucewa, dan haka sun ci gaba da yi wa mazauna garuruwa sata, sannan su na kokarin kewaye birnin Kyiv.
Sojoji Rasha sun yi wa sojojin da ke kare Irpin ruwan makaman atilari.