Bayan harin da ya kashe mutum 85 tare da raunata wasu da dama a garin Tudun Biri na jihar Kaduna, Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), ta nemi rundunar sojin Najeriya ta sake duba dokokinta na yaƙi da matsalar tsaro.
Wani jirgi maras matuƙi na runduar sojin ƙasa ta Najeriya ne ya jefa wa mutanen bam suna tsaka da bukukuwan Mauliidi a yankin ƙaramar hukumar Igabi ranar Lahadi.
Shugaban sashen yaɗa labarai na ofishin kare haƙƙin ɗan’adam na MDD, Seif Magango, ya yi tir da harin yana mai cewa shi ne na baya-bayan nan daga cikin aƙalla huɗu da suka kashe fararen hula tun 2017.
“Duk da cewa gwamnati ta ce kuskure ne, muna kira gare su da su yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan fararen hula da dukiyoyinsu a nan gaba,” a cewar Magango cikin wata sanarwa.
“Dole ne su sake duba dokokin kai hari da kuma tsarin aiki don tabbatar da cewa ba a sake maimaita irin wannan ba.”