Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin Isra’ila sun sake buɗe wuta kan Falasɗinawa da ke cikin tsananin buƙatar agaji a kusa da inda ake rabon kayan tallafi a cibiyoyi biyu, a jiya Lahadi.
Asibitoci a Gaza sun ce aƙalla Falasdinawa 27 aka kashe.
Rahotanni na cewa sojojin sun buɗe wa mutane wuta bayan isa gab da ɗaya daga cikin cibiyoyin rabon agajin na gidauniyar da Amurka da Isra’ila ke mara wa baya a Rafah.
Sanan sauran kuma an kashe su ne a sansanin da ke tsakiyar Gaza.
Har yanzu sojojin Isra’ila ba su yi martani ba kan wannan rahoton.
Hamas ta ce ƙungiyar agaji ta Red Cross kaɗai za ta iya miƙa wa ‘yan Isra’ilar da take riƙe dasu a Gaza idan har aka cimma daidaituwar ba da dama a shigar da kayan agaji a duk sassan zirrin.