Ma’aikatar tsaron Isra’ila (IDF) ta ce an harba rokoki kusan 30 zuwa cikin ƙasar daga Lebanon, kuma ta kakkaɓo wasu daga ciki.
Tun da farko a wani sako a shafin Telegram, IDF ta ce ta kakkaɓo “rokoki da yawa” da aka harba cikin ƙasarta daga Lebanon – bayan samun gargaɗi daga yankin Galilee da ke aewacin ƙasar.
Kafin haka, IDF ta ce wani jirgi mara matuki ya ratsa cikin Isra’ila daga Siriya, inda kuma ya faɗi a wani yanki.
Ta ce sojojin saman ƙasar sun samu nasarar kakkaɓo ɗaya daga cikin jiragen, inda ɗayan kuma ya lalata wani gini a Herzliya da ke Tel Aviv.