Kafin safiyar yau, an ci gaba da gwabza fada a Kibbutz Kfar Azza, daya daga cikin garuruwan Isra’ila da ke kan iyaka da Gaza.
Hakan ce ta sa sai yanzu ne suke tattara gawawwakin ‘yan Isra’ilan da aka kashe lokacin da Hamas ta keta shingen wayar karfe daga Gaza.
Yayin da muka nufi Kfar Azza, har a lokacin ana tura sojoji mayakan Isra’ila zuwa filayen da ke kewaye da kibbutz.
Ana jin amon makamai masu sarrafa kansu da suka kalli cikin iyakar Gaza. Sun ce suna ruguje wani gini bayan hango kai-kawo a hawa na biyu na gini.
Sojojin akasari sun fito ne daga rundunonin wucin gadi. Wani jami’i wanda ya ce shi mahaifin ‘ya’ya shida ne ya amsa cewa al’ummar Isra’ila na tsananin rarrabuwar kai ta fuskar siyasa – amma ya dage a kan cewa yanzu sun hada kai saboda an kawo musu hari.