Kafofin yaɗa labaran Iran sun ambato rundunar sojin ƙasar ne cewa harin da Isra’ila ta kai ƙasar cikin dare ya kashe dakarunta biyu.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar, IRNA ya wallafa sanarwar sojin da ke cewa: ”Dakarun Jamhuriyar Musulunci da ke aikin tsaro da kare mutanen Iran, sun sadaukar da dakarunsu biyu da ke ƙoƙarin kare ƙasarmu daga gwamnatin Yahudawa da ke aikata miyagun laifuka”.