Rundunar hadin gwiwa mai yaƙi da Boko Haram a Tafkin Chadi MNJTF ta ce, ta yi nasarar kashe kwamandan ƙungiyar da mayaƙansa biyar.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Laraba ta ce dakarunta sun fafata da mayaƙan ne a yankin Koulfoua bayan kai musu hari, inda suka kashe kwamandan mai suna Amir Dumkei da wasu ‘yanbindiga biyar.
“‘Yanta’addan ne suka fara kawo hari da farar safiyar Talata a sansanin sojan MNJTF da ke Koulfoua, amma kuma sai suka hadu da ruwan wutar da ya fi ƙarfinsu,” a cewar sanarwar da Kanal Olaniyi Osoba ya fitar.
Ta ƙara da cewa ta ƙwace makamai da dama a hannunsu da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 tara, da ƙananan jiragen ruwa uku, da ƙunshin harsasai mai girma.