Rundunar sojin Burkina Faso ta ce, ta kashe masu ikirarin jihadi akalla 128 a wani samame da sojojinta suka kai.
Ta ce an kara tsaurara hare-hare da ake kaiwa ta sama da ta kasa, tsakanin tsakiyar watan Mayu zuwa tsakiyar watan Yuni.
Burkina Faso dai ta sha fama da hare-haren masu ikirarin jihadi akai-akai tun shekarar 2015.
A watan da ya gabata mahara sun kai farmaki garin Seytenga da ke Arewacin yankin Sahel, inda suka kashe mutane sama da 80 tare da raba dubbai da matsugunansu.
A watan Janairu ne sojoji suka kwace mulki a wani juyin mulki, inda suka dora alhakin hakan a kan gazawar gwamnati wajen magance matsalar rashin tsaro. In ji BBC.