Jami’an ‘yan sandan jihar Legas, sun kama wasu sojoji hudu na bogi, bayan da aka kama motar da suke ciki a unguwar Iju a jihar ranar Lahadi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ne ya sanar da kama shi a wata gajeriyar sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya lissafa sunayen wadanda ake zargin sun hada da maza uku da mata daya kamar haka Samuel Abel, Victor ljeemai, Lukman Salabiu da kuma
da Oyinyechi Macus.
Ya ce, “Jami’an Iju Divison karkashin jagorancin DPO, CSP Gbenga Stephen, a yau da misalin karfe 1:30 na safe sun kama wasu sojoji hudu na bogi a yankin Iju na jihar Legas. Sojojin jabun da aka kama a cikin wata mota kirar Mazda3 saloon su ne Samuel Abel ‘m’ 28, Victor ljeemai ‘m’ 35, Lukman Salabiu ‘m’ 43 1/2 da Oyinyechi Macus ‘f’ 30.
“An tura su zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, Yaba don ci gaba da bincike.”