Rundunar sojoji ta ce, ta kaddamar da bincike kan kisan da aka yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.
Mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar ta biyu ta Operation Hadin Kai, Kennedy Anyawu, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Damaturu. In ji BBC.
Rundunar ta ce tuni ta kama sojoji biyu, kofur John Gabriel da kofur Adamu Gideon a kan batun kisan malamin.
Rundunar da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ne za su gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Kazalika rundunar ta kuma kafa wani kwamiti da zai bankado yadda lamarin ya auku.
Idan aka kammala bincike aka gano wadanda suka aikata kisan to lallai za su fuskanci hukunci da ya kamata in ji rundunar.
Kisan malamin É—an Jihar Yobe ya ja hankalin ‘yan Æ™asar musamman ma’abota shafukan zumunta.
A ranar Juma’ar da ta wuce ne aka kashe malamin a lokacin da yake tuÆ™a motarsa a kan hanyar zuwa Gashua daga Nguru.


