fidelitybank

Sojoji sun yi wa ƴan bindiga ƙwantan ɓauna a Kaduna

Date:

Rundunar Sojoji da ke aiki da rundunar ‘Operation Whirl Punch’ mai yaƙi da masu garkuwa da mutane sun kashe ‘yan bindiga biyar a yankin Dantarau da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Cikin wata sanarwa da kwamishin tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ya ce dakarun sojin waɗanda ke aiki a yankunan ƙananan hukumomin Kachia da Kajuru sun kuma ƙwato makamai.

”Sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu, da bindiga ƙirar gida guda ɗaya, ƙwason zuba alburushi na Ak-47 guda tara, da harsasai 250 da babura biyu da wayoyin oba-oba biyu”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun kuma lalata sansanonin ‘yan bindigar a yankin Sabon Birnin Daji da ke ƙaramar hukumar Igabi.

Aruwan ya kuma ce a lokacin samamen sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar lamarin da ya sa wasu da dama daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Kan hakan ne Aruwan ya yi kira ga mazauna yankunan ƙaramar hukumar Igabi su sanya idanu kan mutanen da za su gani da raunukan bindiga.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp