Rundunar sojoji karkashin Operation Hadin Kai, ta bayyana cewa sun kashe ‘yan Boko Haram da dama yayin da suka kai farmaki kan sansanonin ‘yan ta’adda guda shida da ke gefen dajin Sambisa a jihar Borno.
Wasu majiyoyin leken asiri da dama sun shaidawa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya a tafkin Chadi cewa, an kawar da ‘yan ta’addan ne bayan da dakarun ta 21 Task Force Brigade Bama, tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force, (CJTF), a jiya suka yi kutse cikin ‘yan ta’addan.
Sojojin sun yi nasarar kawar da maboyar ‘yan ta’addan da ke Bula Agaida; Bula Yaga; Bula Lambai; Kuluri; Bula Umar da New Churchur a karamar hukumar Bama a jihar Borno.
Karanta Wannan: Ƴan Boko Haram 51,828 ne suka miƙa wuya ga gwamnati – Irabor
An kuma tattaro cewa, a yayin farmakin sojojin sun gano tare da lalata wani babban sansanin ‘yan Boko Haram.