Jami’an tsaron hadin gwiwa sun yi nasarar kashe fitaccen shugaban ‘yan bindigar da aka fi sani da “Ba bakin-baƙo” tare da mayakansa a dajin Batsari da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.
Sojojin Najeriya, ‘yan sanda, jami’an tsaron farin kaya da Civil Defence, NSCDC, da ‘yan banga – CWC ne suka gudanar da ayyukan.
Wani fitaccen shugaban ‘yan fashi da makami da ke da alhakin kai munanan hare-hare da garkuwa da mutane da ya addabi al’umomi da dama a jihar Katsina, Bako-baƙon ya dade yana cin karo da jami’an tsaro.
Ana ɗaukar mutuwarsa a matsayin babban ci gaba a ƙoƙarin yaƙi da ‘yan fashi a yankin.