Rundunar sojin saman Najeriya ta ce, ta kashe ƴan bindiga masu yawa a yayin wasu hare-hare ta sama da ta ƙaddamar kan maɓoyar ‘yan ta’adda a wasu sassan ƙasar nan.
Cikin wata sanarwar da rundunar ta fitar ranar Lahadi, mai ɗauke da sa hannun daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ta ce dakarun sojin ƙarƙashin haɗin gwiwar rundunonin Hadin Kai da ta Hadarin Daji sun kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a Bukar Meram, kusa da Tafkin Chadi a jihar Borno da kuma yankin Sangeko a jihar Zamfara.
Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce rundunar ta ƙaddamar da hare-haren ne bayan da ta samu bayanai game da sauya matsuguni da ‘yan bindigar ke yi.
Harin farko an kai shi a lokacin da ‘yan bindigar ke ƙaura daga Suwa zuwa yankin Bukar Meram, domin shirya kai hare-hare kan fararen hula da sojoji, kamar yadda sanarawar ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewa harin ya samu nasarar halaka ‘yan ta’addan masu yawan gaske tare da lalata babura fiye da 40 da motocin da ke dakon makamai ga ‘yan bindigar.
Haka kuma Gabkwet ya ce sojojin ƙarƙashin rundunar Hadarin Daji, sun ƙaddamar da makamancin irin wannan hari ranar 11 ga watan Oktaba a yankin Sangeko da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Ya ƙara da cewa dakarun sun kai hari kan ‘yan ta’addan waɗanda ke tafiya cikin jerin gwanon babura kimanin 70 a kan hanya daga Kabaro zuwa Sangeko, inda aka kashe da dama da jikkata wasu,tare da lalata babura masu yawa.