Sojojin Najeriya sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok mai suna Ruth Bitrus da aka yi garkuwa da ita tare da wasu da dama daga makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati ta Chibok da ke Jihar Borno a ranar 14 ga Afrilu, 2014.
Dakarun Sojoji na 21 masu sulke a garin Bama na jihar Borno, sun ceto Ruth da danta a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, bayan ta kubuta daga hannun ‘yan Boko Haram da ke yankin karamar hukumar Bama ta jihar.
A cikin wani faifan bidiyo da Zagazola Makama, masani a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi ya fitar, Ruth ta ce, ta tsere daga dajin Sambisa shekaru takwas bayan da ‘yan ta’addar Boko Haram suka sace ta daga makarantarta da ke garin Chibok.
Ta ce, dan ta’addan da ya shigar da ita ciki, ya kai harin ne da bom a lokacin da yake kokarin tayar da shi a kan dakarun Operation Hadin Kai da ke Arewa maso Gabas.
Ta kara da cewa har yanzu sauran ‘yan matan makarantar na tare da wadanda suka yi garkuwa da su a dajin Sambisa.