fidelitybank

Sojoji sun tarwatsa ‘yan kungiyar awaren IPOB da ESN

Date:

Rundunar sojin kasar nan tare da haɗin gwiwar dakarun Task Force Tactical Patrol Squad, sun kai wani samame a wani sansanin horas da masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) da takwararta ta ESN a unguwar Ihechiowa dake ƙaramar hukumar Arochukwu ta jihar Abia.

A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar kutsawa tare da tarwatsa sansanin da kuma lalata dukkan na’urorin horas da mayaƙan da kuma kayayyakin da aka samu a wurin.

A cikin wata sanarwa da da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce, samamen da sojojinta suka kai wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da ake yi na daƙile ayyukan ta’addanci da ƙungiyoyin IPOB da ESN ke yi, waɗanda ke da alaka da kalubalen tsaro da tashe-tashen hankula da ake fama da su a kan ‘yan ƙasa da ba su ji ba su gani ba da kuma jami’an tsaro a jihar.

Baya ga lalata sansanin ƴan awaren, sojojin sun kuma kai hari kan gine-ginen da ake amfani da su a matsayin maɓoya ga manyan kwamandojin ESN.

Farmakin dai na zuwa ne bayan yadda ‘yan ta’addan IPOB da ESN ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da hukumomin gwamnati a jihar Abia da ma wasu sassan Kudu maso gabashin kasar nan.

 

 

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp