fidelitybank

Sojoji sun tarwatsa wajen da ake hakar man fetur ba bisa ka’ida ba a Rivers

Date:

Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, NNS, Pathfinder, ta tarwatsa wasu wuraren tace, matatun ba bisa ka’ida ba, a karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni dake jihar Ribas, a ci gaba da kokarin dakile satar danyen mai da ayyukan tudun mun tsira.

Aikin ya bankado tanda 45, da tafkunan ruwa 30, da ramuka 75, wadanda ke dauke da kimanin lita 60,000 na danyen mai da ake zargin an sace da lita 80,000 na man fetur da ake zargin an tace ba bisa ka’ida ba, AGO.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamandan NNS Pathfinder, Commodore Cajethan Nnabuchi Aniaku.

A cewar Aniaku, aikin da aka gudanar a ranar 12 ga watan Mayun 2025, ya kuma kai ga lalata lita 33,000 na kananzir.

Ya ce, kungiyar Tactical Riverine Assault Squadron Team ta gano wasu rijiyoyi guda biyu da ke da alaka da bututun mai da ake kyautata zaton barayin mai na amfani da shi wajen dibar danyen mai zuwa sansanonin su.

Aniaku ya lura cewa kayayyakin da aka kama an gudanar da su ne bisa ka’idojin hana satar danyen mai.

Ya kara da cewa ba a kama wani mutum ba, domin wadanda ake zargin sun gudu ne bayan da suka hango tawagar sojojin ruwa da ke gabatowa.

Ya yaba da jajircewa da kwarewa na ma’aikatansa tare da jaddada kudurin sojojin ruwan Najeriya, karkashin jagorancin Vice Admiral E.I. Ogalla, don magance satar danyen man fetur da barasa ba bisa ka’ida ba, ayyukan da ya bayyana a matsayin babbar barazana ga tattalin arzikin kasa da tsaron makamashi.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp