fidelitybank

Sojoji sun tarwatsa sansanin dan fashin daji Yellow Janbros a Zamfara

Date:

Rundunar soji ta ce, dakarunta da ke aikin dakile ayyukan ta’addanci sun kai samame tare da tartwatsa sansanin wani kasurgumin dan fashin daji mai suna Yellow Janbros a kauyen Dangunu da ke karamar hukumar Maru na jihar Zamfara.

Sanarwar da sojojin suka fitar a shafin X, ta ce sun samu nasarar kashe wani da suka kira ɗan ta’adda yayin samamen.

Sojojin sun ce ɗan fashin dajin ya kware wajen yin garkuwa da mutane da kuma aikata ta’addanci a sassan arewa maso yamma yayin samamen da suka kai ranar Litinin, 8 ga watan Afrilun 2024.

“Sojojin sun ci karfin ‘yan fashin dajin inda suka samu nasarar kashe daya daga cikinsu,” in ji sanarwar sojojin.

Sun kuma ce sun kwato makamai da suka haɗa da bindigar AK-47 guda ɗaya, da harsasai da kuma buhunan hatsi 150 da ‘yan bindigar suka sace.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp