Rundunar sojin kasa ta ce dakarunta sun tarwatsa wuraren da ake zargin shalkwatar dakarun rundunar tsaro ta gabashin Najeriya, wadda ke aiki a matsayin rundunar ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra ta IPOB.
Shalkwatar rundunar sojin Najeriya ta wallafa hotunan cibiyar da ta tarwatsa, inda ta nuna irin abubuwan da ta samu a wuraren.
Shalkwatar Sojin ta ce, ta kai samame ne a cibiyar rundunar ESN a tsibiran da suke kananan hukumomin Orsu da Ihiala na jihar Imo da kuma Anambra.
Ta kuma ce bayanan sirri da ta tattara sun nuna cewa daga cibiyoyin ne kungiyar ke kitsa duk wani mummunan aiki da take gudanarwa a ƙarƙashin ESN.