Rundunar Sojoji ƙarƙashin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ mai yaƙi da ta’addanci, sun kashe mayaƙan Boko Haram 24 a wani mummunan hari da suka ƙaddamar kan maɓoyarsu a yankin raewa maso gabashin Najeriya.
Mataimakin dakartan hulda da jama’a na rundunar, Captain Reuben Kovangiya ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Captain Kovangiya ya ce cikin wadanda aka kashe har da mutum biyar da ke samar wa mayaƙan makamai, waɗanda aka yi wa kwanton-ɓauna a wani samame da sojojin suka ƙadamar cikin dare.
Sanarwar ta ce sojojin sun ƙaddamar hare-haren ne dajin Sambisa da yankin Timbuktu da tsaunukan Mandara da wasu wurare, tun daga ranar 4 zuwa 9 ga watan da muke ciki.
Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato makamai da alburusai da wasu kayyakin yaƙin ƙungiyar ta Boko Haram.