fidelitybank

Sojoji sun samu galaba a kan Kasurgumin dan fashin dajin Zamfara

Date:

Hukumomi a Najeriya sun ce, sun tarwatsa sansanin wani ƙasurgumin ɗan fashin daji da ya addabi sassan jihohin Zamfara da Katsina, tare da gomman yaransa.

Rundunar sojin saman ƙasar ta tabbatar wa BBC cewa, an kashe Halilu Tubali da yaransa a wani hari da jirgin yaƙi da dakarunta suka kai a ƙarshen makon jiya.

Majiyoyi sun ce yana ɗaya daga cikin shugabannin ‘yan fashin daji da suka fi kuɗi, kuma ya ƙware wajen fasa-ƙwaurin makamai.

Hukumomin sun ce sun samu labarin cewa wannan kasurgumin dan fashin daji yana gudanar da wani taro ne tare da yaransa masu yawa, ko da yake dama sun dade suna fakonsa, da wuraren da yake mu’amalarsa.

Ka zalika an tarwatsa wani rumbun ajiyar makaman Tubali a wannan hari, kamar yadda daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin sama air kwamado Edward Gabkwet, ya bayyana mani.

Sai dai bayanan da na tattaro daga yankin na Muradun sun nuna cewa akai-akai ‘yan bindigar ke yin taruka domin tsara yadda za su rika kai hari kan al’umma ko kuma jami’na tsaro.

Duk da dai babu wani cikakken adadin mutanen da aka kasha ko aka jikkata, amma ta tabbata an lalata sansanin Halilu Tubali wanda hakan a cewar rundunar sojin saman ka iya samar da kwanciyar hankali a yankin na Zamfara da Katsina ganin mummunan tasirin da yake da shi ya yankin.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp