fidelitybank

Sojoji sun raraki Lakurawa sun kuma fice daga Najeriya – Adamu Aliero

Date:

Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero, ya ce sojojin Najeriya sun samu nasarar fatattakar ƴan Lakurawa, inda suka tsallaka zuwa Nijar.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Aliero ya ce an samu nasarar ne bayan ɗaukar matakin da ministan tsaro Abubakar Bagudu da babban hafsan tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suka ɗauka, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Aliero ya ce, “mun faɗa wa ministan cewa idan aka yi sakaci da ƴanta’addan Lakurawa, za a iya maimaita abin da ya faru a arewa maso gabas a arewa maso yamma. Yaƙi ne da za a iya gamawa a kwana biyar, amma idan aka yi sakaci, lamarin zai ƙazance saboda yankin arewa maso yamma ya fi yawan mutane kuma ya fi arziki da ma girman ƙasar noma da kiwo.

“Amma kun san da sojoji suka zo a ranar Talata (12 ga Nuwamba) sun samu nasarar fatattakarsu zuwa Jamhuriyar Nijar?”

Ƴan Lakurawa sun kashe mutane da dama a jihar Kebbi, lamarin da ya sa Sanata Aliero da sauran ƴan majalisar jihar suka kai ziyara a ƙananan hukumomin Argungu da Augie domin gane wa idonsu irin ɓarnar da suke yi.

nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp