Dakarun runduna ta ɗaya ta sojin kasar nan ta kashe wasu ‘yan bindiga shida tare da kama wasu mutum uku a wani samame na musamman da ta kai ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce, sojojin sun samu nasarar kakkaɓe ‘yan bindigar bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ta’addanci a yankin Galadimawa na karamar hukumar Giwa.
Sojojin sun kwato shanu tare da miƙa su ga mutanen yankin.
Daga nan ne sojojin suka hango maharan a dandalin kasuwar Galadimawa.
Bayan ƙaddamar da bincike a yankin ne kuma sojojin suka kama wasu mutum uku da ake zargi da hada baki tare da bai wa ‘yan bindigar bayanai.
Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato babura biyu tare da wayoyin hannu huɗu a lokacin gumurzun.